Kasar Sin ta bukaci a yi kokarin mayar da yarjejeniyar nukiliyar Iran bisa turba
2020-12-23 12:30:29 CRI
Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD, Geng Shuang, ya yi kira da a yi kokarin mayar da yarjejeniyar nukiliyar Iran bisa turba, yana mai kira ga kasar Amurka ta gaggauta komawa yarjejeniyar.
Geng Shuang, ya ce yarjejeniyar nukiliyar Iran, muhimmiyar nasara ce ga tsarin diflomasiyyar kasa da kasa da ta samu amincewar kuduri na 2231 na kwamitin sulhu na MDD, haka kuma tana da karfin doka, don haka ya kamata a aiwatar da ita yadda ya kamata.
Ya ce janyewar Amurka daga yarjejeniyar a watan Mayun 2018, da ci gaba da matsawa Iran lamba da kuma lahanta kokarin dukkan bangarori dake girmama yarjejeniyar da take yi, su ne tushen haddasa yanayin da ake ciki yanzu dangane da yarjejeniyar. (Fa’iza Mustapha)
Labarai Masu Nasaba
- Kasar Sin ta yi kira ga Amurka ta gaggauta komawa yarjejeniyar nukiliyar Iran
- Kasar Sin ta samu nasarori a fannin raya birane
- Shugaban Iran ya ce a shirye yake ya sake komawa yarjejeniyar nukiliya idan sauran bangarorin sun amince
- Iran: takunkuman Amurka sun datse hanyar samun da biliyan 50 na ribar musayar kudade