logo

HAUSA

Iran ta yi kira da dakarun sojin ketare da su fice daga yankunanta

2020-12-29 10:17:53 CRI

Sakataren hukumar koli ta tsaron kasar Iran Ali Shamkhani, ya yi kira ga dakarun sojojin kasashen ketare da su fice daga yankunan kasar, yana mai cewa, za a iya cimma nasarar samun cikakken tsaro a yankin ne, idan kasashen ketare suka tsame hannunsu daga harkokin yankin.

Kamfanin dillancin labarai na FARS, ya rawaito Ali Shamkhani na cewa, karin dakarun Amurka da ake gani a baya bayan nan a yankin, alamu ne dake nuni ga bijirewa doka da haifar da yanayin fargaba.

Kafin hakan, shi ma kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh, ya bayyana cewa, Iran ta mikawa Amurka sakon gargadi, na kauracewa ci gaba da kutse a yankin.

Khatibzadeh ya ce, Iran ba ta fatan ganin an shiga halin dar dar a yankin, sai dai kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare kan ta. Ya ce Iran na fatan Amurka za ta fuskanci gaskiya, ta kauracewa rura wutar tashin hankali a yankin. (Saminu)