logo

HAUSA

Iran ta kara yawan sunayen Amurkawan da take zargi da hannu a kashe Soleimani zuwa 48

2020-12-28 10:57:47 CRI

Rahotanni daga kasar Iran na cewa, mahukuntan kasar sun kara yawan sunayen Amurkawan da kasar ke zargi da hannu, wajen halaka babban kwamandan dakarun juyin juya halin kasar, Qassem Soleimani zuwa sunaye 48.

Da yake yiwa taron manema labarai karin haske, game da matakan doka da kasar za ta dauka kan kisan kwamandan nata, mai magana da yawun kwamitin dake tunawa da shahidi janar Soleimani, Hossein Amin Abdollahian, ya bayyana fatan ganin kotu ta yanke hukunci nan ba da dadewa ba. Yana mai cewa, Iran ta aikawa kasashe shida sammacin kama wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

A ranar 3 ga watan Janairun shekarar 2020 ne, wani hari ta sama da aka kai a kusa da filin jiragen saman kasa da kasa dake Badagaza ya halaka Soleimani, kwamandan dakarun kurdawan juyin juya halin Islama na Iran.

Bayan kisan nasa ne, kasar Iran ta bukaci hukumar ‘yan sanda ta duniya, da ta kama jami’an Amurka 36, ciki har da shugaba Donald Trump na Amurka, bisa zarginsa da hannu a kisan Soleimani.(Ibrahim)