logo

HAUSA

Jami’in UNECA: AfCFTA ita ce hanyar da za ta kai Afirka ga samun dauwamammen ci gaba

2020-12-25 11:09:41 CRI

Babban jami'in cibiyar kula da manufofin cinikayyar Afirka (ATPC) na hukumar kula da tattalin arzikin Afirka na MDD wato UNECA David Luke, ya bayyana cewa, ya kamata a sakarwa yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta Afirka (AfCFTA) mara ta yi aiki yadda ya kamata, kasancewarta hanya mafi dacewa ga nahiyar ta samun dauwamammen ci gaba.

Jami’in ya bayyana haka ne, yayin da yake jawabi ta kafar bidiyo, game da fannonin da yarjejeniyar ta shafa. Yana mai cewa, “ bai kamata mu yi wasa da fa’idojijin dake kunshe cikin wannan yarjejeniya ba, yana mai jaddada cewa, babu shiri na biyu dake tafe, don haka, kamata ya yi mu yi kokarin ganin yarjejeniyar ta kankama.

Luke ya kuma jaddada cewa, kowa ce al’umma tana samun ci gaba ne, lokacin da jama’ar suka fadada karfinsu na samar da kaya, da inganci aiki da takara, ta hanyar cinikayya, kuma Afirka ba za ta zama saniyar ware ba.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya