logo

HAUSA

Kwararru na maraba da matakin bude kan iyakokin Najeriya gabanin fara aiki da yarjejeniyar AfCFTA

2020-12-18 09:38:10 CRI

Kwararru a fannin hada hadar cinikayya, sun jinjinawa matakin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauka, na sake bude kan iyakokin ta na tudu, gabanin fara aiki da yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta kasashen Afirka ko AfCFTA a takaice.

Tun da fari, an tsara fara aiki da yarjejeniyar ne daga watan Yulin bana, amma aka dage zuwa 1 ga watan Janairun shekarar 2021 dake tafe, sakamakon barkewar cutar COVID-19.

Masana na ganin bude kan iyakokin Najeriya zai ba da damar bunkasa hada hadar cinikayya, musamman wadanda ke dogaro da safarar hajoji ta tudu.

Game da dalilin rufe kan iyakokin kasar har tsawon watanni 16 kuwa, ministar kudi da tsare tsare ta kasar Zainab Ahmed, ta ce shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin garkake iyakokin ne a wani mataki dakile ayyukan ‘yan fasakwauri.  (Saminu)