logo

HAUSA

Najeriya ta gabatarwa AU takardar shaidar amincewa da shiga AfCFTA

2020-12-06 21:14:36 CRI

A yau Lahadi Najeriya ta gabatarwa kungiyar tarayyar Afrika AU tabbacin amincewarta na shiga yankin ciniki marar shige ta nahiyar Afrika wato AfCFTA a takaice.

A ranar Asabar ne kasar ta mika takardar bayanan nuna amincewarta da yarjejeniyar shiga yankin, gabanin fara amfani da tsarin cinikayyar cikin ‘yanci a tsakanin kasashen nahiyar wanda zai fara aiki daga wata mai zuwa, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta bayyana.

Wakilin Najeriya a kungiyar AU, Richards Adejola, shi ne ya mika bayanan a madadin kasar. A cewar sanarwar, Najeriya ta mika bayanan ne da nufin daga matsayin harkokin cinikayya a tsakanin nahiyar Afrika da kuma kara inganta dunkulewar kasashen nahiyar.(Ahmad)