logo

HAUSA

AU ta bayyana cinikayya karkashin AfCFTA a matsayin cikar mafarkin nahiyar

2020-12-07 10:50:59 CRI

Hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta jaddada cewa, burin nahiyar ya cika, bayan da shugabannin kasashen nahiyar suka amince da yin harkokin cinikayya karkashin yarjejeniyar yankin cinikayya maras shinge ta Afirka (AfCFTA) da zarar ta fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2021.

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat wanda ya bayyana haka, ya jaddada cewa, sabon ci gaban da aka samu game da wannan yarjejeniya, tamkar cikar burin da iyayen da suka assasa kungiyar hadin kan Afirka(OUA) ne suka dade suna fatan gani, wadanda a kullum suke da burin samar da kasuwar Afirka ta bai daya.

Jagororin nahiyar sun nanata kudirinsu na kara dunkulewar nahiyar ta hanyar yarjejeniyar, sun kuma yaba gudummawar da ministocin cinikayya na nahiyar suka bayar, wajen shirya kaddamar da cinikayya a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2021.

Yayin bikin da ya gudana ta kafar bibiyo, shugaban karba-karba na kungiyar Tarayyar Afirka na wannan karo, kana shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya bayyana cewa, fara harkokin cinikayya, zai kasance daya daga cikin zakaran gwajin dafi mai muhimmanci a aikin dunkulewar nahiyar, da share fagen kokarin nahiyar na inganta makomarta, da har yanzu take fafutuka.

Ramaphosa ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wata muhimmiyar kafa, da za ta kai ga cika mafarki da burin dunkulewar nahiyar waje guda.(Ibrahim)