logo

HAUSA

AfCFTA zata samar da sabon cigaban zamani a Afrika

2020-12-06 16:35:47 CRI

Jagoran kungiyar tarayyar Afrika AU, Cyril Ramaphosa, ya ce yarjejeniyar yankin ciniki maras shinge ta nahiyar Afrika wato AfCFTA, wata alama ce ta samar da sabon cigaban zamani ga nahiyar Afrika.

A jawabin da ya gabatar a taron kolin AU karo na 13, wanda shugabannin kungiyar suka gudanar ta kafar bidiyo, domin tattauna batun yankin AfCFTA da batutuwan dake shafar tashe tashen hankula a nahiyar, Ramaphosa ya ce, cinikayya karkashin tsarin yarjejeniyar AfCFTA wadda za ta fara daga ranar 1 ga watan Janairu daya ne daga cikin muhimman alamun dake nuna dunkulewar nahiyar.

Ramaphosa ya bukaci bangarori masu zaman kansu da su shiga wannan tsari ta hanyar zuba jari na kudade da kuma ginin kayayyakin more rayuwa.

A cewar Ramaphosa, yankin ciniki maras shinge na AfCFTA zai bunkasa tsarin gamayyar bangarori daban daban.

Ya kara da cewa, za kuma a yi amfani da yarjejeniyar wajen bunkasa cigaban mata da kuma baiwa matan damammakin shiga harkokin kasuwanci.(Ahmad)