logo

HAUSA

Shugaban Iran ya ce a shirye yake ya sake komawa yarjejeniyar nukiliya idan sauran bangarorin sun amince

2020-12-15 14:06:27 CRI

A ranar Litinin shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta sake shiga yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015 muddin sauran bangarorin da abin ya shafa sun shirya yin hakan.

A wata sanarwar da aka fitar cikin jawabin da shugaban ya gabatar kai tsaye ta gidan talabijin din kasar, Rouhani ya bukaci gwamnatin shugaban Amurka mai zuwa da ta sake dawowa kan yarjejeniyar ta JCPOA da kuma aiwatar da yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun da farko.

Rouhani ya ce, gwamnatinsa ba za ta amince Amurka ta ci gaba da tsawaita takunkumin da aka kakabawa kasar Iran bayan cikar wa’adinsa ba.

Manyan kasashen duniya da Iran sun kulla yarjejeniyar JCPOA a shekarar 2015 domin warware batutuwan dake shafar shirin nukiliyar Iran. Sai dai a shekarar 2018, Amurka ta janye daga yarjejeniyar ta JCPOA duk da nuna adawar da dukkannin bangarorin da abin ya shafa suka yi kan matakin na Amurka.(Ahmad)

Ahmad Fagam