logo

HAUSA

Iran: takunkuman Amurka sun datse hanyar samun da biliyan 50 na ribar musayar kudade

2020-12-17 10:43:11 CRI

Kakakin gwamnatin kasar Iran, Ali Rabiee, ya ce takunkuman da Amurka ta kakabawa kasar cikin shekaru 2 da suka gabata, ya hana ta samun kudin da ya kai dala biliyan 50 na ribar musayar kudade.

Kamfanin dillancin labarai na IRNA, ya ruwaito kakakin na cewa, sun gamu da matsalolin samun kayayyakin da za a sarrafa domin samar da magunguna da kayyakin aiki na masana’antu.

A cikin shekarar 2018 ne shugaban Amurka Donald Trump, ya janye kasarsa daga yarjejeniyar kasa da kasa kan nukiliyar Iran tare da mayar da tsoffin takunkumai har ma da sabbi da suka shafi kudi da makamashi kan kasar, a wani yunkuri na matsawa Iran din shiga wata sabuwar tattaunawa game da yarjejeniyar ta 2015, bukatar da Iran din ta ki amincewa da ita. (Fa’iza Mustapha)