Kasar Sin ta samu nasarori a fannin raya birane
2020-12-22 11:15:16 CRI
Ministan kula da gidaje da raya birane na kasar Sin, Wang Menghui, ya ce kasar ta cimma gagarumar nasara a fannin gini da raya birane, bisa amfani da sabon ingantaccen tsarin raya birane yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 13 tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.
Yayin wani taro kan ayyukan kasa da aka yi jiya, ministan ya ce daga watan Janairu zuwa Nuwamban bana, an sanya tsoffin unguwannin birane 39,700 cikin jerin wadanda za a yi wa kwaskwarima, aikin da iyalai kusan miliyan 7.25 suka ci gajiya, a yayin da kasar ke kokarin inganta yanayin rayuwa a tsoffin unguwanni.
A shekarar 2019, fadin kowanne gida a birane ya tsaya kan murabba’in mita 39.8 yayin da na karkara ya tsaya kan murabba’in mita 48.9.
Ministan ya yi kira da a kara kokarin inganta raya birane a 2021, domin samar da birane masu juriya da nagarta dake kyautata muhalli da raya al’adu. (Fa’iza Mustapha)