logo

HAUSA

Na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5 ta dawo duniyarmu tare da samfurori daga duniyar wata

2020-12-17 14:31:58 CRI

Da karfe 1 da minti 59 na safiyar yau Alhamis 17 ga wata ne, bangaren dawowa na na’urar binciken duniyar wata kirar Chang’e-5, ya sauka a daidai wurin da aka tsara a yankin Siziwangqi da ke jihar Mongolia ta Gida a arewacin kasar Sin, lamarin da ya alamta cewa, kasar Sin ta samu nasarar kammala aikin tattaro samfuri daga wata duniya ta daban, da kuma dawo da shi duniyarmu karo na farko.

Zhang Kejian, babban kwamandan aikin binciken duniyar wata, kuma shugaban hukumar nazarin sararin samaniya ta kasar Sin ya sanar da nasarar gudanar da aikin a hukumance. Na’urar binciken duniyar wata kirar Chang’e-5 ta dawo gida bayan yin ziyara ta tsawon kwanaki fiye da 20.

Bayan saukowar na’urar a doron kasa ba tare da wata matsala ba, masu nazarin kimiyya sun same ta kan lokaci, sun kuma fara ayyuka masu nasaba da hakan. Wu Yanhua, mataimakin shugaban hukumar nazarin sararin samaniya ta kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, yau an samu nasarar dawo da na’urar Chang’e-5. Lallai, yau an samu cikakkiyar nasara fiye da yadda ake zato. Inda ya ce,“Yau an ci nasarar ayyuka. Da farko, mun samu nasarar gudanar da ayyukan da suka shafi na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5, mun kuma samu nasarar kammala matakai guda 3 na binciken duniyar wata, wato zagaya wata, sauka kan wata da kuma dawowa daga wata. Nasarar da muka samu, gaggaruma ce, kuma ta kasance tamkar wata gada dake hade baya da kuma gaba. Na biyu kuma samfurorin da kasar Sin ta dauko daga duniyar wata, samfurori ne masu wuyar samuwa ga masu kimiyya na kasar Sin, da na kasa da kasa. Za su amfani masu binciken sararin sama, da kuma dasa harsashin ayyukan da za su biyo baya, dangane da binciken duniya ta daban.”

An yi karin bayanin cewa, bayan da aka dauki wasu matakai masu nasaba da aikin dawowar na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5, za a kai ta Beijing, hedkwatar kasar Sin cikin jirgin sama, inda za a bude ta, za a dauki nau’oin samfurin, da kuma abubuwan da ke cikin na’urar.

Hukumar nazarin sararin samaniya ta kasar Sin za ta shirya wani biki a lokacin da zai dace, inda za a mika samfuroin duniyar wata a hukumance. Sa’an nan kuma karo na farko, kasar Sin za ta kaddamar da ayyukan ajiye samfurorin da aka tattaro daga wata duniya ta daban, da nazari da dai sauransu. Hu Hao, babban mai kula da ayyukan binciken duniyar wata a mataki na 3 ya yi bayani da cewa, "Yau na gamsu da yadda na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5 ta sauka a daidai wurin da aka tsara a baya. A kan hanyarta ta dawowa duniyarmu, a lokacin da nisan da ke tsakanin na’urar da kuma doron kasa ya kai kilomita 10, na’urar ta bude laimar sauka. Daga nan, wurin saukar na’urar ya dogara ne da kadawar iska. Ko da yake ban samu bayanai ba tukuna, amma a gani na, na’urar ta sauka daidai wurin da aka tsara. Mun dauki matakai duka a tsanake. Mun cimma manufofinmu da muka tsara a baya duka. ”

Na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5 ta kammala ayyukan tattaron samfuri daga duniyar wata, ta sauko daga duniyar wata zuwa duniyarmu tare da samfuri, da wasu ayyuka daya bayan daya a wannan karo. Ta kafa tarihi a kasar Sin a fannin nazarin sararin samaniya. Ta dasa aya ga shirin kasar Sin na binciken duniyar wata cikin matakai guda 3 cikin nasara, wato zagaya wata, da sauka kan wata, da dawowa daga wata.

Haka zalika kuma, aikin na’urar Chang’e-5 ya zama aikin nazarin sararin samaniya na kasar Sin mafi sarkakkiya da wuya. Ya kuma samu babban ci gaba a wasu muhimman fannoni. Don haka ya kasance wata gada dake hade baya da kuma gaba wajen daga matsayin kasar Sin na nazarin sararin samaniya, da kyautata tsarin ayyukan binciken duniyar wata, da kaddamar da nazarin duniyar wata, da fara tsara ayyukan da suka biyo baya, dangane da nazarin duniyar wata da kuma wata duniya ta daban. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan