logo

HAUSA

Na'urar Chang'e-5 ta yi kewaye na biyu a falakin ta

2020-11-26 11:34:45 CRI

Na'urar Chang'e-5 ta yi kewaye na biyu a falakin ta

Na’urar binciken duniyar wata ta Chang'e-5 kirar kasar Sin, ta yi kewaye na biyu a falakin ta a daren jiya Laraba. Hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Sin CNSA, ta ce kafin hakan, na’urar ta yi tafiyar kusan sa’o’i 41 kan falakin ta, ta kuma baiwa doron duniya tazarar kilomita kusan 270,000. Kuma dukkanin sassan na’urar na aiki yadda ya kamata.

CNSA ta kara da cewa, na’urorin doron duniya, da cibiyoyin sadarwa masu nasaba da wannan aiki, wadanda ke musayar bayanai da sarrafa na’urar ta Chang'e-5, na gudanar da aikin su yadda aka tsara.  (Saminu)

Saminu Alhassan