logo

HAUSA

Zhong Nanshan: Ya Kamata A Ci Gaba Da Yaki Da Cutar COVID-19 Ta Hanyoyin Kimiyya Da Fasaha

2020-12-10 11:18:53 CRI

Zhong Nanshan: Ya Kamata A Ci Gaba Da Yaki Da Cutar COVID-19 Ta Hanyoyin Kimiyya Da Fasaha

A kwanakin baya ne, aka shirya wani taron dandalin tattaunawar kimiyya da fasaha na kasa da kasa a birnin Beijing. A yayin taron, kwararren injiniya na kasar Sin Zhong Nanshan ya bayyana cewa, kasar Sin ta cimma sakamako mai gamsarwa kan aikin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, bisa tushen yin hadin gwiwa tsakanin dukkanin al’ummomin kasar kan ayyukan kandagarki da hana yaduwar cutar COVID-19. An kuma cimma wannan nasara ce, saboda yadda aka yi amfani da hanyoyin kimiyya da fasaha wajen warware matsalolin dake shafar kwayar cutar numfashi ta COVID-19.

Babban taken wannan taro shi ne “kimiyya da fasaha da kalubalolin kasa da kasa”, wanda ya samu halartar wadanda suka lashe kyautar lambobin yabo ta Nobel guda 10, da kwararru a fannin kimiyya da aikin injiniya na kasar Sin da na kasashen ketare guda 30, da wasu wakilan kungiyoyin kimiyya da fasaha guda 300.

Wadanda suka lashe kyautar lambobin yabo ta Nobel a fannoni daban daban da suka hada da Randy W. Schekman, da Michael Kosterlitz da kuma Michael Levitt da sauransu, sun yi jawabai game da ayyukan gaggawa masu tsanani dake shafar al’umma, da kara ilimantar da jama’a game da harkokin kimiyya da fasaha, da karfafawa yara da matasa gwiwa na sha’awar harkokin kimiyya da fasaha da sauran batutuwa.

A nasa jawabin, shugaban babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana fuskantar matsalar siyasantar da batun kimiyya da fasaha, a don haka ya kamata kafofin yada labarai na kasa da kasa, su tsaya tsayin daka wajen yada ra’ayoyi da harkokin da suka shafi kimiyya da fasaha yadda ya kamata, domin su ne muhimman hanyoyin da al’ummomin kasa da kasa suke samun labaran kimiyya da fasaha da sauransu. Ya kara da cewa, CMG zai ci gaba da dukufa wajen yada harkokin kimiyya da fasaha yadda ya kamata, domin ba da gudummawa wajen kara ilimantar da al’umma game da harkokin kimiyya da fasaha. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)