logo

HAUSA

Sin Tana Kokarin Yin Kirkire-kirkire A Fannin Kimiyya da Fasaha

2020-12-05 16:40:35 CRI

Sin Tana Kokarin Yin Kirkire-kirkire A Fannin Kimiyya da Fasaha

A kwanakin baya, hotuna da bayanai da dama game da na’urar bincike ta Chang’e-5 dake gudanar da ayyukan bincike a duniyar wata sun jawo hankalin jama’a daga sassan duniya sosai. An ce, wannan ne karo na shida da Sin ta tura na’urar bincike zuwa duniyar wata, kana shi ne aiki mafi wuya a tarihin binciken sararin samaniya na kasar Sin, kuma karo na farko a tarihi.

Kafin hakan, na’urar binciken teku mai zurfi ta Fendouzhe ta kafa sabuwar bajinta, wato ta sauka tare da daukar mutane da yin nutso cikin teku mai zurfin mita 10909 yayin da take gudanar da aikinta a karo na 13, wannan ya alamta cewa, Sin ta kai matsayin farko a duniya a fannin shiga teku mafi zurfi.

Daga binciken duniyar wata a sararin samaniya, zuwa shiga teku mai zurfi, da kuma bunkasa fasahar sadarwa ta 5G, Sin tana kokarin yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha da kuma samun babban ci gaba a wannan fanni.

A hakika dai, a shekarun baya baya nan, Sin ta kara zuba jari ga nazari da bincike a fannin kimiyya da fasaha, wanda yawansu ya karu daga Yuan biliyan 71.6 a shekarar 2015 zuwa Yuan biliyan 133.56 a shekarar 2019, karuwar kashi 16.9 cikin dari a duk shekara. Kana yawan kirkire-kirkiren da Sin ta yi ya kai matsayin na 15 dake kan gaba a duniya a shekaru 2 a jere, don haka Sin ta zama kasa mai salon kirkire-kirkire a duniya.

Koda yake Sin ta samu nasarori a fannin bunkasa kimiyya da fasaha, amma akwai gibi da dama a tsakaninta da kasashe masu ci gaba a wannan fanni, ya kamata Sin ta ci gaba da kokarin kirkire-kirkire tare da shiryawa tunkarar kalubale.

A gun cikakken zama na 5 na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin karo na 19, an gabatar da manufofin kiyaye kirkire-kirkire, da maida shi matsayi mafi muhimmanci wajen zamanintar da kasar a dukkan fannoni, kuma bunkasuwar kimiyya da fasaha ta nuna goyon baya ga raya kasar. Kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin ya gabatar da manufofin don shaida cewa, samun ci gaba bisa kirkire-kirkire na da muhimmanci sosai.

Ban da wannan kuma, ya kamata a daidaita dangantakar dake tsakanin aikin bunkasa kimiyya da fasaha da bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa. Sin ba ta rufe kofa da samun ci gaban kirkire-kirkire da kanta ba, don haka ya kamata a samar da wani tsarin hadin gwiwa na yin kirkire-kirkire a duniya, da inganta karfin kasar tare da koyon fasahohi daga kasashen waje, da kuma kara hadin gwiwa a wannan fanni don kara samar da gudummawar Sin, kamar sabon shirin Sin da kuma sabon tunanin Sin ga duniya. (Zainab Zhang)