logo

HAUSA

Aikin binciken duniyar wata a mataki na 4 zai samar da abubuwan bukata don gina tashar binciken duniyar wata

2020-11-26 15:52:24 CRI

Babban jagoran tsara shirin binciken duniyar wata na kasar Sin Wu Weiren, ya ce aikin binciken duniyar wata a mataki na 4 da kasar za ta aiwatar, zai samar da abubuwan bukata, na gina tashar binciken duniyar ta wata.

Wu ya bayyana hakan ne, yayin taron dandalin kasa da kasa game da ayyukan sama jannati na shekarar 2020 da aka rufe a ranar Talata a birnin Wenchang, inda ya ce, ayyukan da za a yi, sun hada da kafa na’urorin bincike masu kewaya falaki, da kuma doron duniyar watan.

A cewar sa, za a yi amfani da kayayyakin wajen tantance bayanai don gane da abubuwan dake da nasaba da binciken kimiyya da fasaha a fannin, da bunkasa albarkatu, da kuma amfani da su. Kaza lika za su taimaka wajan samar da damar yin hadin gwiwa da sassan kasa da kasa, wajen gina tashar binciken duniyar wata ta kasa da kasa.  (Saminu)

Saminu Alhassan