logo

HAUSA

Kungiyar malaman makarantu a Najeriya ta yi barazanar shiga yajin aiki sakamakon karuwar barazanar tsaro

2020-12-16 13:29:59 CRI

Kungiyar malaman makarantu a Najeriya NUT, ta yi barazanar shiga yajin aiki, sakamakon karuwar barazanar farwa makarantun kasar.

Cikin wata sanarwa da NUTn ta fitar, ta ce harin baya bayan nan da aka kaiwa makarantar sakandaren gwamnati dake Kankara a jihar Katsina, na nuni ga irin hadari da dalibai, tare da malaman suke ciki a makarantun kasar.

NUT ta ce, "bisa halin da ake ciki a yanzu, za a dakatar da harkokin koyarwa, har zuwa lokacin da za a samu tabbacin tsaron lafiyar ‘yan makaranta da malalai, ba tare da tsoron yin garkuwa da su, daga mahara dake yiwa harkar ilimin kasar kafar ungulu ba”.

A wani ci gaban kuma, kungiyar ta yi kira ga daukacin sassan gwamnatoci a dukkanin matakai, da su fara aiwatar da tsarin sanya ido na ko da yaushe kan makarantun dake kasar.   (Saminu)

Saminu Alhassan