logo

HAUSA

Gwamnan jihar Katsina a Najeriya ya rufe dukkan makarantun kwana bayan harin ‘yan bindiga

2020-12-13 16:20:53 CRI

Gwamnan jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya a jiya Asabar ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun sakandaren kwana na jihar ba tare da bata lokaci ba.

Aminu Masari, gwamnan jihar Katsina, ya bayar da wannan umarni ne bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu daga cikin daliban makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati wato GSSS dake garin Kankara a daren Juma’ar da ta gabata.

Masari, ya roki al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, kana ya ba da tabbacin cewa, gwamnatin jihar za ta yi dukkan abin da ya dace domin tabbatar da ganin an kubutar da daliban da aka yi garkuwar da su.

Sama da daliban makaranta ta GSSS 200 ne suka koma makarantar, kamar yadda hukumar ‘yan sandan yankin ta tabbatar da hakan.

Mafi yawan daliban sun haura katangar makarantar ne suke tsere cikin daji da sauran wurare dake makwabtaka da makarantar domin neman mafaka a lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin, a cewar Gambo Isah, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho.

Rahotanni sun bayyana cewa, mai yiwuwa ne an yi garkuwa da wasu daga cikin daliban a lokacin da ‘yan bindigar suka kaddamar da harin wanda suka shafe tsawon sa’a guda.

Gambo Isah ya ce, jami’an ‘yan sanda da hukumar makarantar suna ci gaba da aikin tare domin tantance hakikanin daliban da har yanzu ba su dawo cikin makarantar ba.(Ahmad)