logo

HAUSA

An rufe makarantu 10 a Najeriya sakamakon garkuwa da yan makaranta

2020-12-16 10:36:46 CEI

Kimanin makarantu 10 aka rufe a jahar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, wacce ke makwabtaka da jahar Katsina inda aka sace dalibai ’yan makaranta sama da 300 bayan wani hari na baya bayan nan da ’yan bindiga suka kaddamar a makarantar.

Ibrahim Abdullahi, kwamishinan ilmin jahar Zamfara, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, makarantun na cikin yanayin barazanar fuskantar hare-haren ’yan bindiga, kuma an dauki wannan mataki ne domin kiyaye lafiyarsu, musamman makarantun dake yankuna masu makwabtaka da sauran jihohin arewa maso yammacin kasar.

Kwamishinan ilmin ya ce, sun samu amincewar gwamnan jihar Bello Matawalle na rufe dukkan makarantun dake yankuna masu makwabtaka da jahohin Kaduna da Katsina, bayan garkuwar da aka yi da yara ’yan makarantar sakandaren kimiyya ta Kankara sama da 300 a jahar Katsina. (Ahmad)