logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya yi Allah wadai da harin da aka kai makaranta

2020-12-13 20:15:41 CRI

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da ‘yan bindiga suka kaddamar a makarantar sakandare a jihar Katsina dake shiyyar arewa maso yammacin kasar, kana ya umarci hukumomin tsaro da su binciko maharan kuma su tabbatar an kubatar da dukkan yaran ba tare da salwata ko kuma jikkata ko da yaro guda ba.

A ranar Asabar shugaba Buhari ya kuma bayar da umarnin tura jami’an tsaro ga dukkan makarantu karkashin tsarin gwamnati na kiyaye tsaron makarantun, matakin na zuwa ne bayan harin da ‘yan bindiga suka kaddamar a ranar Juma’a a makarantar sakandaren kimiyya ta GSSS ta garin Kankara dake jihar.

A wata sanarwa, shugaban na Najeriya ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da ‘yan bindigar suka kaddamar kan yara ‘yan makarantar sakandaren kimiyya ta garin Kankara, shugaban ya yi alkawarin ci gaba da baiwa jami’an ‘yan sandan kasar da sojojin taimako a kokarin da suke na yaki da ‘yan ta’adda da barayi ‘yan bindiga.

Buhari ya ce sojojin kasa, tare da hadin gwiwar dakarun tsaron sama na kasar, sun yiwa ‘yan bindigar kawanya a maboyarsu dake dajin Zango-Paula dake garin Kankara, kuma suna ci gaba da musayar wuta da barayin.(Ahmad)