logo

HAUSA

An samu karin mutane 418 da suka kamu da COVID-19 a Najeriya

2020-12-15 12:24:43 CRI

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta sanar a ranar Litinin cewa, an samu sabbin mutane 418 da suka kamu da cutar COVID-19 cikin sa’o’i 24 da suka gabata, adadin da ya kai jimillar mutane 73,175 da suka kamu da cutar a fadin kasar.

Haka zalika, an samu sabbin mutane 3 da cutar ta kashe, inda yawan mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar a duk fadin kasar ya kai 1,197.

Tattalin arzikin Najeriya ya samu koma baya a karo na biyu cikin shekaru hudu sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya sanadiyyar barkewar annobar COVID-19, kamar yadda hukumar kididdigar kasar ta sanar a watan Nuwamban bana.(Ahmad)

Ahmad Fagam