logo

HAUSA

Iran ta cafke wasu dake da hannu a kisan da aka yi wa babban masanin nukiliyar kasar

2020-12-09 10:29:24 CRI

Hukumomin tsaron Iran, sun gano tare da cafke wasu mutane dake da hannu a kisan da aka yi wa babban masanin nukiliyar kasar.

Kamfanin dillancin labarai na ISNA, ya ruwaito mashawarcin shugaban majalisar dokokin kasar, Hossein Amr-Abdollahian na tabbatar da hakan, yana mai cewa, wadanda ke da hannu a kisan ba za su taba kaucewa fuskantar hukunci ba.

Babban masanin kimiyyar nukiliya na kasar Iran, Mohsen Fakhrizadeh, ya mutu ne sanadiyyar raunika masu tsanani a asibiti a ranar 27 ga watan Nuwamba, biyo bayan wani hari da wasu masu dauke da makamai suka kai wa motarsa a lardin Absard, dake da nisan kilomita 60 daga arewa maso gabashin Tehran.

Iran dai na zargin Isra’ila da aikata kisan. (Fa’iza Mustapha)

jamila