Iran na adawa da sake nazarin yarjejeniyar nukiliyarta
2020-12-08 12:54:03 CRI
Ma’aikatar harkokin wajen Iran, ta ce yarjejeniyar nukiliyar kasar na da matukar muhimmanci, don haka, kasar na adawa da batun sake nazarinta.
Yayin wani taron manema labarai da aka yi a jiya, kakakin ma’aikatar Said Khatibzad ya kuma yi kira ga wasu kasashen Turai da su daina watsi da tanade-tanaden yarjejeniyar.
Kakakin ya mayar da martani ne ga jawabin ministan harkokin wajen Jamus, Heiko Josef Maas kan batun yarjejeniyar. Rahotannin sun ruwaito Ministan na Jamus na cewa, akwai bukatar sake nazarin yarjejeniyar domin cimma karin matsaya, da kuma sanya takunkumi kan shirin nukiliyar Iran. (Fa’iza Mustapha)
Labarai Masu Nasaba
- Iran za ta kara yawan man da take hakowa da fitarwa zuwa ketare
- An cimma burin tsabtar ruwa a dukkan birane da garuruwan jihar Xinjiang
- Kasashen duniya sun yi Allah wadai da kisan masanin kimiyar nukiliya na kasar Iran
- Iran ta yi Allah wadai da kashe babban masanin nukiliyarta yayin da kasa da kasa ke nuna damuwa kan lamarin