Iran ta ki yarda da sake nazarin yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015
2020-12-09 13:38:05 CRI
A jiya Talata gwamnatin Iran ta bayyana yin watsi da yiwuwar sake cimma matsaya kan yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015, wacce aka fi sani da JCPOA.
Ita dai wannan yarjejeniya ta JCPOA, an gudanar da cikakkiyar tattaunawa kanta a shekaru biyar da suka gabata kuma ba ta bukatar sake cimma matsaya kanta, a cewar Ali Rabiei, kakakin gwamnatin Iran, wanda ya bayyana haka a yayin wani taron manema labarai.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauki mataki na kashin kansa inda ya janye Washington daga yarjejeniyar ta JCPOA a shekarar 2018, kana ya sake kakabawa Iran takunkumai.
Duk da cewa alamu suna nuna yiwuwar sabon shugaban Amurka da aka zaba Joe Biden zai iya komawa cikin yarjejeniyar, amma masu taimaka masa da wasu daga cikin shugabannin kasashen Turai suna yin kiraye kirayen a sake cimma matsaya domin kara sanya takunkumi kan shirin nukiliyar Iran da shirinta na kera makamai masu linzami.(Ahmad)