Ministan harkokin wajen Iran: dawo cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran shi ne nauyin dake wuyan Amurka
2020-12-11 13:27:57 CRI
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewa, ya kamata kasar Amurka ta dawo cikin yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, ta kuma dauki nauyinta na ganin an aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.
Ya kara da cewa, kasar Amurka ta keta hakkin al’ummomin kasar Iran, duk da cewa, Amurka ba ta cimma burinta ba, amma matakin ta ya kuntatawa jama’ar kasar Iran matuka. A don haka, ya yi kira da a warware wannan matsala, domin cimma moriyar juna.
Kwanan baya, batun ko kasar Amurka za ta dawo cikin yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran bayan Joseph Biden ya kama aiki, ya janyo hankulan kasa da kasa. (Maryam)