logo

HAUSA

Dakarun Nijeriya sun kashe mayakan BH 20

2020-12-14 12:39:33 CRI

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe mayakan BH akalla 20, yayin da suke kokarin dakile wani hari da kungiyar ta kaddamar a yankin arewa maso gabashin kasar.

An dakile harin ne a yankin karamar hukumar Askira-Uba dake arewacin jihar Borno, a lokacin da mayakan BH suka yi kokarin farwa fararen hula.

Ado Isa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kashe soja guda yayin da wasu biyu kuma suka jikkata yayin musayar wuta.

Mayakan da ake zargin sun fito daga dajin Sambisa, sansaninsu mafi girma a Nijeriya, cikin manyan motoci, sun doshi yankin Askira-Uba daga bangarori daban-daban a lokaci guda, da niyyar kai hari.

Sojoji sun kuma kwato motocin yaki 4 yayin da aka lalata wasu da dama yayin luguden wuta ta sama da aka yi da taimakon sojojin kasa. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha