logo

HAUSA

Fashewar wasu motoci ta yi sanadin mutuwar mutane 4 da jikkatar wasu a Nijeriya

2020-12-12 16:57:53 CRI

Kungiyar Agaji ta Red Cross reshen Nijeriya, ta tabbatar da cewa, mutane akalla 4 sun mutu, wasu 8 kuma sun jikkata, sanadiyyar fashewar wasu abubuwa cikin motoci 2 a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Kakakin kungiyar agaji ta Red Cross Aliyu Dawobe, ya ce lamarin ya auku ne a garin Dikwa dake da nisan kilomita 90 daga birnin Maiduguri, inda wasu abubuwa da ake zargin bama bamai ne, suka fashe a cikin wasu motoci biyu.

Kawo yanzu dai, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin aukuwar lamarin. (Fa’iza Mustapha)