logo

HAUSA

‘Yan bindinga sun farwa wata makaranta a arewacin Nijeriya

2020-12-12 20:46:07 CRI

Wasu gungun ‘yan bindiga da ba san ko su wane ne ba, sun kai hari wata makarantar sakandare dake jihar Katsina, a arewacin Nijeriya, inda suka dauke wasu dalibai.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Gambo Isa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce wasu tsageru sun kai hari makarantar sakandare ta gwamnati ta maza, dake garin kankara na jihar.

Ya ce tsagerun sun kai harin ne da misalin karfe 11 na dare a jiya, amma ba su kai ga tantance adadin daliban da aka dauke ba.

Ya ce an tura jami’an ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro a yankin. (Fa’iza Mustapha)