logo

HAUSA

An yi kiyasin yawan al’ummar Nijeriya ya kai miliyan 206

2020-12-09 09:55:08 CRI

Hukumomi a Nijeriya sun yi kiyasin yawan al’ummar kasar ya karu zuwa miliyan 206.

Shugban hukumar kula da yawan al’umma na kasar Nasir Kwarra ne ya bayyanawa manema labarai hakan a jiya, inda ya ce biyo bayan rashin kidaya, sun yi hasashe, inda suka yi kiyasin cewa, a bana, yawan al’ummar kasar ya tsaya kan miliyan 206.

A shekarar 2018, hukumar ta yi kiyasin yawan al’ummar kasar ya kai miliyan 198. Kiyasin na baya-bayan nan, ya nuna cewa akwai yiwuwar an samu karuwar miliyan 8.

Bisa la’akari da cewa, an yi kidaya a kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika kafin shekaru 14 da suka gabata, abu ne mai wahala a san ainihin adadin al’ummar a yanzu. (Fa’iza Mustapha)