logo

HAUSA

Gwamnan jihar Bornon Nijeriya na neman mayar da ‘yan gudun hijirar jihar 200,000 gida daga kasashe makwabta

2020-12-12 15:58:23 CRI

Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya, Babagana Umara Zulum, ya ce ya na neman hadin kan gwamnatin tarayya domin mayar da kimanin ‘yan gudun hijirar jihar 200,000 dake watangarari a kasashen Niger da Kamaru da Chadi dake makwabtaka da kasar.

Yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da yarjejniyar kasa da kasa kan ‘yan gudun hijira a Abuja, Gwamna Umara Zulum, ya nemi taimako daga gwamnatin tarayya, domin mayar da ‘yan gudun hijirar, wadanda rikicin ‘yan ta’adda na kungiyar BH suka tilasta musu tserewa zuwa makwabtan kasashe.

Da yake bayyana taron a matsayin wanda ya cancanci yabo, ya ce yana rokon taimakon gwamnatin tarayya. Kuma gwamnatin jihar a shirye take ta hada hannu da gwamnatin ta hannu ma’aikatar kula da harkokin jin kai ta kasar.

Tun cikin watan Oktoba gwamnatin jihar Borno ta bayyana shirinta na sake tsugunar da karin ‘yan gudun hijira, duk da ci gaba da kai hare-hare da mayakan BH ke yi a jihar. (Fa’iza Mustapha)