logo

HAUSA

Sama da yara ‘yan makaranta 300 ne suka bace bayan farmakin ‘yan bindiga a Katsina

2020-12-14 12:52:40 CRI

Mahukunta a jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya, sun tabbatar da batan yara ‘yan makaranta su 333, bayan harin ‘yan bindiga a makarantar sakandaren gwamnati ta Kankara dake jihar a daren ranar Juma’a.

A jiya Lahadi ne gwamnan jihar Aminu Masari, ya tabbatar da batan ‘yan makarantar, yayin da ya karbi bakuncin mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro Babagana Monguno a Katsina.

Gwamnan ya ce makarantar da ‘yan bindigar suka farwa, na da jimillar dalibai 839, kuma yaran da maharan suka yi awon gaba da su sun fito ne daga sassan jihar daban daban, da ma wasu ‘yan sauran jihohin kasar.

Ya ce bisa alkaluman da aka tattara, yanzu haka ana neman yara 333 ne, wadanda ko dai sun tsere cikin dajin dake daura da makarantar, ko kuma sun koma gidajen iyayen su. Tuni kuma aka baza jami’an tsaro domin bin sawun maharan.

A wani ci gaban kuma, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da harin ‘yan bindigar, yana mai umartar jami’an tsaro da su tabbatar da gano dukkanin yara ‘yan makarantar da suka bace lami lafiya.  (Saminu)

Saminu Alhassan