logo

HAUSA

Sabon Tsarin Ci Gaba Na Kasar Sin Zai Kara Hadin Kanta Da Duniya Don Samun Bunkasuwa Tare

2020-11-20 10:38:46 CRI

Sabon Tsarin Ci Gaba Na Kasar Sin Zai Kara Hadin Kanta Da Duniya Don Samun Bunkasuwa Tare

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron shawarwarin shugabannin masana’antu da cinikayya na kungiyar APEC ta kafar bidiyo tare da gabatar da jawabi, inda ya sake nanata sabon tsarin ci gaban kasar, ya ce, wannan tsari ba kawai ya shafi kasuwa a gida ba, har ma yana kara bude kofa ga kasashen waje, yana kokarin raya kasuwa a gida da waje a lokaci guda. Dadin dadawa, Xi ya bayyana yadda wannan tsari zai taimakawa duniya daga manyan fannoni uku, wato kasuwanni da bude kofa ga ketare da hadin kai, matakin da ya baiwa duniya damar kara fahimtar bunkasuwar kasar Sin.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kafa wannan sabon tsari ya dogaro da halin da Sin take ciki yanzu tare da yin la’akari da yanayin dunkulewar kasa da kasa da yadda duniya take fuskantar sauye-sauye. Ya ce, an iya fitar da boyayyen karfin kasuwannin kasar Sin don samar da karin dammammaki ga kasashen duniya, Sin za ta kara bude kofarta ga ketare don more zarafin samun bunkasuwa da al’ummar duniya baki daya, Sin kuma za ta kara yin hadin kai da kasashen duniya da kawo moriyar juna da samun bunkasuwa tare, wadannan manyan matakai uku, sun bayyana niyyar Sin ta ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya da samun bunkasuwa tare da sauran kasashe.

A matsayinta na mai goyon bayan hadin kan kasashen nahiyar Asiya da yankin tekun Fasifik, Sin tana kara hada kai da sauran kasashe a kokarin cimma burin yin ciniki cikin ‘yanci tsakanin kasashen nahiyar Asiya da yankin tekun Fasifik, ta yadda za su taka rawa wajen kara azama kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya. (Amina Xu)