logo

HAUSA

An gudanar da taron dandalin kafofin watsa labarun Sin da Afirka a Kenya

2020-11-19 13:28:44 CRI

An gudanar da taron dandalin kafofin watsa labarun Sin da Afirka a Kenya

 

Kwanan baya, an yi taron dandalin kafofin watsa labarun Sin da Afrika a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, mai taken “Hadin kan Sin da Afrika a zamanin amfani da yanar gizo”. Jami’ai da manema labarai da masana kimanin 120 daga Sin da sauran kasashen Afrika 11 sun halarci taro da ya gudana ta kafar bidiyo.

Shekarar 2020, shekaru 20 ke nan da kafa dandalin tattaunwar hadin kan Sin da Afrika, manufar taron da aka kira a wannan karo, ita ce tabbatar da ci gaban da aka samu a taron koli na Beijing da aka yi a shekarar 2018, da kuma habaka hadin kan Sin da Afrika a fannin watsa labarai.

An gudanar da taron dandalin kafofin watsa labarun Sin da Afirka a Kenya

Tian Yuhong, sakataren kungiyar manema labarai ta kasar Sin ya yi jawabi cewa, Sin da Afrika na samun ci gaba mai armashi a fannin watsa labarai karkashin jagorancin dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika. Ya kuma ba da shawara cewa, kamata ya yi Sin da Afrika su kara yin mu’ammala da hadin kai da yin koyi da juna, don kokarin cimma burin raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya, ta yadda za su ingiza bunkasuwar kafofin yada labarai cikin hadin kai. Ya ce:

“Amurka da wasu kasashen yamma, sun dade suna baza jita-jita kan Sin da Afrika da yunkurin tada rikici tsakaninsu ta amfani da fifikonsu a fannin yada labarai don kiyaye moriyarsu, da shafa bakin fenti kan hanyar da Sin da Afrika ke bi na samun bunkasuwa da manufofi da ci gaban da suka samu. Wannan yanayi ya kara tsananta bayan barkewar cutar COVID-19. A don haka, kamata ya yi, kafofin yada labaran Sin da Afrika su kara hada kai don yada labaran gaskiya da kara fahimtar juna da inganta zumuncinsu. Kungiyar manema labarai ta kasar Sin tana fatan kara hadin kai da kungiyoyin manema labarai na Afrika, don bullo da sabbin hanyoyi da tsare-tsaren horar da ’yan jarida da yin musanyar ra’ayi a wannan fanni.”

Gwaro Ogaro, wakilin mataimakiyar ministan kula da fasahohin sadarwa ta kasar Kenya Maureen Mbaka, ya ce, kafofin watsa labaru na Afrika na kokarin bayyana labarai da ra’ayin Afrika ta dandaloli masu amfani da fasahar yanar gizo. Yanzu gwamnatin kasar na kokarin inganta fannin yanar gizo ta yadda al’umma za su rugumi wannan fasaha a koda yaushe, ya ce:

“Yayin da muke murnar cika shekaru 20 da kafuwar dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika, wannan taro ya zama muhimmin dandali wajen zurfafa hadin kan kasashen biyu. Dangantakar Sin da Afrika na kara bunkasa a matsayin mambar nahiyar Afrika, Kenya tana taka rawa don kara dankon zumuncin dake tsakanin bangarorin biyu, tare kuma da cin gajiyarsa. Taron ya dace da manufofin diplomasiyyarmu kuma ya samar da wata dama, ta musayar ilimi da kwarewar da za ta inganta aikin jarida.”

Jakadan Sin dake Kenya Zhou Pingjian ya nuna cewa, a cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, dandalin tattaunwar hadin kan Sin da Afrika, ya samar da wani tsari da zai taimakawa fannin hadin kansu, kuma ya zama abin misali ga hadin kan kasashe masu tasowa. Sin tana tsayawa tsayin daka wajen sauraron ra’ayi da mutunta muradu da kuma biya bukatun Afrika.

Zhou Pingjian yana mai fatan wannan taro, zai samar da wani nagartaccen yanayin ga aikin yada labarai. Ya ce:

An gudanar da taron dandalin kafofin watsa labarun Sin da Afirka a Kenya

“Juyin juya halin masana’antu karo na hudu, wanda ya kunshi fasahohi na zamani da sauransu, ya bullo da wani sabon babi ga kasashen Sin da Afirka. Tun bayan barkewar wannan mummunar cuta, kafofin yada labarai da dama na gaggauta bunkasa fasahar yanar gizo. Muna fatan kafofin yada labarai za su kara taka rawa wajen zamanintar da masana’antun Afrika da kara hadin kan Sin da Afrika.”

Rahotanni na cewa, jami’ai da kuma ’yan jarida kimanin 120 daga Sin da kasashen Afrika 11 sun halarci wannan taro da ya gudana ta kafar bidiyo. Ban da wannan kuma, mahalarta taron sun tattauna kan wasu manyan batutuwa dangane da fasahohin yada labarai ta yanar gizo da sauransu, kazalika kimanin mutane dubu sun kalli wannan taro ta yanar gizao (Amina Xu)