Xi Jinping: A rika kirkiro sabbin fasahohi don bunkasa tattalin arziki
2020-11-19 14:03:13 CRI
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron shugabannin fannonin masana’antu da kasuwanci na kungiyar APEC, wato kungiyar hadin kan tattalin arzikin Asiya da tekun Pasific, a yau Alhamis, inda ya jaddada cewa, kasar Sin na kallon aikin kirkiro sabbin fasahohi a matsayin bangare mafi muhimmanci da ke taimakawa raya tattalin arzikin kasar. Saboda haka, Sinawa suna kokarin hada bangarorin kimiyya da fasaha, da aikin ilimi, da masana’antu, da hada-hadar kudi waje guda, don inganta tsare-tsaren masana’antun a kai a kai, ta yadda za a iya tabbatar da makomar tattalin arzikin kasar mai haske. (Bello Wang)