logo

HAUSA

Xi Jinping: Sin ba ta dakatar da bude kofa ga kasashen waje ba yayin da ake fuskantar karuwa ra’ayin bada kariya ga cinikayya

2020-11-19 12:04:47 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron shawarwarin shugabannin masana’antu da cinikayya na kungiyar APEC ta kafar bidiyo tare da gabatar da jawabi, inda ya yi nuni da cewa, a wannan shekarar da muke ciki, kasar Sin maimakon ta dakatar da bude kofarta ga kasashen waje, ta gabatar da karin wasu manufofi na bude kofarta ga kasashe daban daban.

Ya ce bude kofa yana daga cikin manufofin kasar na samun ci gaba, yayin da rufe kofa babu abin da zai haifar sai koma baya. A don haka kasar Sin ta riga ta shiga tsarin tattalin arzikin duniya da tsarin kasa da kasa. Sin ba za ta fice daga harkokin kasa da kasa ba, kuma ba za ta rufe kofarta da ma kin amincewa da sauran kasashe ba.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin za ta kara kokari tare da gabatar da karin matakai, don kawar da abubuwan dake kawo cikas ga raya tsarin tafiyar da harkokin kasa. Haka kuma kasar Sin tana ba da muhimmanci ga aikin kirkire-kirkire wajen samun ci gaba, matakin da ya dade yana ba da taimako wajen raya tattalin arzikin Sin. Bisa sabon tsarin samun bunkasuwa na yanzu, kasuwar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa don kara biya bukatun kasashen duniya. (Zainab)