logo

HAUSA

Cutar COVID-19 Na Kara Illata Al’Ummar Amurka Saboda Karancin Nagartattun Matakai

2020-11-20 15:53:39 cri

Cutar COVID-19 Na Kara Illata Al’Ummar Amurka Saboda Karancin Nagartattun Matakai

Kwanan baya, masanin kiwon lafiya na jami’ar Georgetown mista Lawrence Goldstein ya yi gargadi cewa, al’ummar Amurka za ta shiga mummunan yanayi a watanni uku masu zuwa kan tinkarar cutar COVID-19.

Ya zuwa ranar 18 ga wata, yawan wadanda suka mutu a kasar sakamakon cutar ya wuce dubu 250, kafar yada labarai ta CNN ta bayyana wannan adadi a matsayin al’amari mai firgitarwa

Abin bakin ciki shi ne, a makon da ya gabata yara da matasa kimanin miliyan 1.04 ne aka tabbatar sun kamu da cutar.

Amma, wadannan alkaluma ba su girgiza zukatan masu mulki a kasar ba, babu abin da suke yi sai harkokinsu na siyasa. Kwanan baya, shugabannin Amurka sun sake shafawa kasar Sin bakin fenti inda suke yiwa wannan cutar lakabin “Kwayar kasar Sin”, don dora laifi kan kasar Sin.

Babban darektan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi gargadi da cewa, kasashe da suka bar cutar tana yaduwa ba tare da daukar matakin da ya dace ba, tamkar suna wasa ne wuta. Kamata ya yi masu mulkin kasar Amurka sun dauki matakan da suka dace ba tare da bata lokaci ba. (Amina Xu)