logo

HAUSA

Pentagon ta tabbatar da janye dakarunta daga Afghanistan da Iraq

2020-11-18 11:13:10 CRI

A ranar Talata helkwatar tsaron Amurka ta Pentagon ta tabbatar cewa zata rage adadin sojojin Amurka dake kasashen Afghanistan da Iraqi zuwa adadin dakaru 2,500 kowannensu ya zuwa tsakiyar watan Janairun 2021.

Mai rikon mukamin sakataren tsaron Amurka Christopher Miller, ya fadawa taron manema labarai a hukumar tsaron Pentagon cewa, ya zuwa ranar 15 ga watan Janairun shekarar 2021, adadin dakarun Amurka dake Afghanistan zai koma sojoji 2,500, sannan yawan sojojin kasar dake Iraqi shi ma zai koma 2,500 a wannan rana.

A halin yanzu, akwai sojojin Amurka kusan 4,500 dake Afghanistan, kana akwai wasu dakarun 3,000 a kasar Iraqi wadanda ke taimakawa sojojin kasashen yakar mayakan IS masu da’awar kafa daular Musulunci, galibin aikinsu shine bayar da horo da kuma shawarwari.(Ahmad)