logo

HAUSA

Ziyarar Mike Pompeo A Kasashe 7 Na Turai Da Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba Ta Samu Maraba Ba

2020-11-17 15:15:59 CRI Hausa

Ziyarar Mike Pompeo A Kasashe 7 Na Turai Da Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba Ta Samu Maraba Ba

Kwanan baya, Mike Pompeo ya gudanar da ziyarar aiki a kasashe 7 dake Turai da yankin gabas ta tsakiya, kamfanin dillancin labarai na AP, ya bayyana wannan ziyara a matsayin “Ziyarar da ba ta samun maraba ba ko kadan”. Ko shakka babu, wadannan kasashe ba za su yi maraba da zuwansa ba.

Da farko bari mu duba matakin da Farasan ta dauka kan ziyarar, wadda ta zama zangonsa na farko. A cewar gidan telibijin na France 24, shugaban kasar Emmanuel Macron ya bayyana cewa, babu abin da za a boyewa tawagar Joseph Robinette Biden a ganawar da ya yi tare da Pompeo ba. Game da batun neman goyon baya daga Faransa kan batun janye sojin Amurka daga gabas ta tsakiya, wanda mai yiwuwa Pompeo zai ambata cikin ganawarsu, ministan harkokin wajen kasar Jean-Yves Le Drian ya ce, bangaren Faransa zai bukaci sojojin Amurka da su ci gaba da zama a kasashen Iraki da Afghanistan.

Zango na biyu shi ne kasar Turkiya. Mike Pompeo ya sha tsoma baki kan batun ‘yancin bin addini a Turkiya kafin wannan ziyara. Bangeren Turkiya ya ba da sanarwa cewa, laifi tudu ne, ka take naka ka hango na wani, kamata ya yi Amurka ta daidaita matsalolinta na hakkin bil Adama. Shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan da ministan harkokin wajen kasar Mevlut Cavusoglu ba su tsai da shirin ganawa da shi ba.

Ban da wannan kuma, ya tsai da wata ziyara mai tada hankali, wato kai ziyara matsugunan Yahudawa da aka mamaye a gabar yammacin kogin Jordan na Palasdinu. Tun lokacin da galibin kasashen duniya suka ayyana matsugunan a matsayin haramtattu, firaministan Palesdinu Mohammed Shtayyeh ya yi Allah wadai da ziyarar tasa, kuma ya bayyana wannan ziyara a matsayin mataki dake sabawa kudurin MDD, wanda kuma aka yi imanin zai aike da mummunan sako ga halasta matsugunan.

Me ya sa Mike Pompeo wanda ya yi kaurin suna a duniya yake son kai ziyara a wadannan kasashe 7 kafin karewar wa’adinsa tare da daukar wasu matakai masu hadari?

Darektan kwalejin nazarin manufofin diplomasiyya da tsaron kasar Amurka Kori Schake ya ce, Pompeo yana son jawo hankalin masu kada kuri’u ta wannan hanya wadda ta kasance mataki na karshe da zai dauka don neman kuri’u a zaben da za a yi a shekarar 2024.

To shin ko irin wannan mataki na rashin hankali zai yi nasara wajen kara karfin siyasa? Da kuma daga sunansa wanda ya riga ya zube sosai a duniya? Ba shakka amsar ita ce a’a.

Ikon da Mike Pompeo ya kafa ta hanyar yin karya, da damfara, da kuma sata yana tabarbarewa. Irin wadannan matakan da ya dauka, ba za su cimma nasara ba, a maimakon haka ma, za su kara bankado halayya da imaninsa marasa kyau. (Amina Xu)