logo

HAUSA

Putin ya yabawa Sin wajen zama abin misali a yaki da cutar COVID-19

2020-11-20 10:47:46 CRI

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a jiya cewa, kasar Sin ta zama abin misali ga kasashen duniya kan yadda ta yi nasarar dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

Shugaba Putin ya bayyana a yayin taron BRICS karo na 12 da Rasha ta dauki bakuncin sa ta kafar bidiyo a ranar Talata cewa, Sin ta riga ta shaidawa duniya cewa, dan Adam yana iya yakar cutar COVID-19. Ya ce, Sin ta samu manyan nasarori wajen hana yaduwar cutar, wadda ta zama abin misali ga kasashen duniya a wannan fanni.

Ya kara da cewa, ya kamata kasashen kungiyar BRICS wato Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin, da kuma Afirka ta Kudu, su kara yin hadin gwiwa wajen yaki da cutar COVID-19. (Zainab)