logo

HAUSA

WHO: Lura ita ce jigon kaucewa bazuwar COVID-19 a Afrika a lokacin hutu

2020-11-20 10:43:16 CRI

WHO: Lura ita ce jigon kaucewa bazuwar COVID-19 a Afrika a lokacin hutu

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bukaci kasashen Afrika su matse kaimi wajen sa ido domin kaucewa karuwar masu kamuwa da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a lokacin hutu.

Daraktar hukumar a nahiyar Matshidiso Moeti ta ce lokacin hutu da ake samun yawan tafiye-tafiye da haduwar iyalai, ka iya mayar da hannun agogo baya dangane da nasarorin da aka cimma na dakile annobar a nahiyar.

Ta yi gargadin cewa, za a iya samun barkewar cutar a cikin wasu rukunoni yayin da ake hutu a yankin kudu da hamadar Sahara, idan al’ummomi suka gaza kiyaye ka’idojin kiwon lafiya dake da nufin dakile bazuwar cutar.

Kididdiga daga cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta nahiyar Afrika, ta ce zuwa jiya Alhamis, yawan wadanda suka kamu da cutar a nahiyar ya kai 2,013,388 yayin da adadin wadanda suka mutu ya kai 48,408. (Fa’iza Mustapha)

Fa'iza Mustapha