Ya ce shugabannin kasashen Afrika na yabawa da shirye-shiryen zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika guda goma, wadanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar ga taron koli na Johannesburg, na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika.
A nasa bangare, Mista Wang ya ce wadannan shirye-shirye da shugaba Xi ya gabatar sun dace da moriyar nahiyar Afrika na raya kansu, kuma su na da ma'ana sosai wajen kara karfin bunkasa kasashen Afrika wajen dogaro da kansu, da karfin tinkarar kalubaloli daga kasashen waje. Ya ce ana fatan kara hadin gwiwa da kasar Mozambique ta fuskar karfin samar da kayayyaki, da sha'anin gona, ta yadda za a kafa wani cikakken tsari na samar da hatsi a Mozambique, sannan kuma a zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta fuskar zaman lafiya da tsaro. (Amina)