A yayin bikin aza tubulin ginin, firaministan kasar Mozambique Carlos do Rosário, ya jinjinawa kasar game da tallafin da take baiwa harkokin kimiya da fasaha. Ya ce Sin sahihiyar abokiyar hadin gwiwa ce ta fuskar kimiyya, kuma abokiyar hadin kai bisa manyan tsare-tsare.
Mr. do Rosário ya kara da cewa, Sin da Mozambique na da dankon zumunci tsakaninsu, kana Sin tana taka rawar gani a Mozambique ta fuskar samar da manyan ababen more rayuwa, da sha'anin noma. Daga nan sai ya gabatar da matukar godiya ga matakin da Sin take dauka na cika alkawarinta a fannin kimiyya.
A cewarsa, yana fatan cibiyar za ta aiwatar da aikinta yadda ya kamata, kuma gwamnatin Mozambique za ta ba da tabbaci ga kididdigar da cibiyar za ta gudanar ta yadda za ta yi amfani ga karin samar da hatsi, da kyautata hidimomin da gwamnati za ta bayar, da kuma hidimomin kiwon lafiya. Dadin dadawa, cibiyar za ta kyautata ayyukan ba da ilmi, don taimakawa gwamnati wajen rage kudin kashewa, da rarraba makamashi yadda ya kamata, da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a.
A tsokacin da ya gabatar jakadan Sin dake kasar Mr. Su Jian, ya ce duba da ci gaban da Sin da Mozambique suke samu wajen hadin gwiwa ta fuskar ciniki da tattalin arziki da tattara kudi, cibiyar za ta sa kaimi ga gudanar da ayyukan gwamnatin Mozambique, ta yadda hakan zai yi amfani ga fannin kimiyya da fasaha, baya ga karfin sadarwa a kasar, hakan zai kuma kawowa al'ummar Mozambique din babbar moriya. (Amina)