in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji a Mozambique sun nuna rashin jin dadi kan zargin su da kai hari
2015-09-16 11:04:26 cri
Rundunar sojan kasar Mozambique ta ce ta nuna rashin jin dadi matuka bisa rahotanni da wasu kafofin yada labarai suka watsa na zargin rundunar da afkawa ayarin motocin babban madugun adawar kasar Afonso Dlhakama a ranar Asabar din nan.

'Yan jaridu a kasar ta Mozambique, sun rawaito cewar an kai harin ne kan tawagar madugun adawar Dhlakama, yayin da yake kan hanyar sa ta dawowa daga wani taron gangamin a lardin Manica.

Wasu kafofin yada labaran kasar sun rawaito cewar maharan jami'an 'yan sandan kwantar da tarzomar kasar ne wato UIR a takaice.

Sai dai rundunar sojan kasar ta yi zargin cewar wasu jami'an diplomasiyya da ke aiki a kasar ne ke kokarin wargaza zaman lafiyar kasar. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China