Gwamnatin kasar Mozambique ta shirya biki a jiya Laraba a Maputo, babban birnin kasar domin karbar tallafin gaggawa da ya kunshi kudade da kayayyaki wadanda darajansu ya kai dalar Amurka dubu 700 da kasar Sin ta samar mata.
Jakadan kasar Sin dake kasar Li Chunhua ya bayyana a gun bikin cewa, an bada da tallafin ne domin taimakawa 'yan gudun hijira dake yankin tsakiya da kuma arewacin kasar Mozambique, da kuma sake tsugunar da mutanen dake fama da bala'in ambaliyar ruwa.
Rork Samuel, mataimakin ministan kula da harkokin al'umma da ma'aikatan gwamnati na kasar Mozambique wanda ya karbi gudunmuwar kayayyakin tallafi a madadin gwamnatin kasar, ya nuna godiya sosai ga taimakon da gwamnati da jama'ar kasar Sin suka bayar cikin gaggawa, tare da yin alkawari cewa, gwamnatin kasar za ta mika wadannan tallafi ga yankuna da jama'a da suka fi bukatar taimako.(Lami)