Babban sakataren babbar kungiyar adawa ta kasar Mozambique ta Renamo, Manuel Bissopo ya bayyana aniyar kungiyar na ci gaba da mallakar makamai domin ta kare kanta daga abin da ta kira abokan gaba.
Bissopo ya bayyana hakan ne a martanin da ya mayar game da kalaman da firaministan Mozamabique Carlos do Rosario ya yi cewa, dakarun tsaron kasar za su ci gaba da kwace makamai daga hannun wadanda ke rika da makamai ba bisa ka'ida ba.
Firaministan dai yana sake nanata jawabin da ministan cikin gidan kasar Jaime Monterio ya yi a ranar Laraba ne cewa, gwamnati za ta kwance damarar makamai daga hannun tsoffin 'yan tawayen Renamo. Matakin da Bissopon ya ce ba za ta sabu ba.
Yarjejeniyar zaman lafiyar da sassan biyu suka cimma a shekarar 1992 a birin Rome ne ta baiwa kungiyar ta Remano 'yancin mallakar mallakan.(Ibrahim)