in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi gagarumar zanga-zanga a Mozambique
2013-11-01 10:43:29 cri
Mutane kimanin dubu 10 ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Maputo, babban birnin kasar Mozambique a ranar 31 ga watan Oktoba nan, domin nuna rashin jin dadinsu, ga tashe-tashen hankulan da suka auku a yan kwanakin baya a kasar, musammman ma kame mutane da aka rika yi.

An ce masu zanga-zangar sun fusata, ganin yadda mahukuntan kasar suka gaza wajen tinkarar wannan rikici, wanda aka ce akwai sa hannun jami'an 'yan sandan kasar cikin lamarin.

Rahotanni sun bayyana cewa, masu zanga-zanga sun nemi shugaban 'yan sandan kasar ya sauka daga mukaminsa.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, kungiyoyi masu zaman kansu dake kasar ne suka jagoranci wannan zanga-zanga, bayan taruwar duban al'umma a filin tunawa da samun 'yancin kan kasar dake cikin birnin Maputo. An dai kammala wannan zanga-zanga cikin lumana, ba kuma a samu rahoton asarar rayuka, ko raunuka ba.

Kafofin yada labaru sun bayyana cewa, karin dalilan da suka haddasa zanga-zangar sun hada da kisan wani mutum, da aka kame a mako da ya gabata a birnin Beira, wanda ke tsakiyar gabar teku. Iyalin mamacin dai na ganin wajibi ne 'yan sanda sun dauki alhakin aukuwar lamarin. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China