A lokacin da yake jawabin yayin bikin rufe gasar da yammacin lahadin data gabata, shugaban kasar Mozambique Armando Guebuza ya jinjinawa 'yan kasar bisa irin dattakon da suka nuna a tsawon makonni biyu da aka shafe ana gudanar da gasar.
Ya ce babu shakka jami`an lura da harkokin wasanni na kasar sun taka rawar ganin wajen shirya wannan gasa, bisa la'akari da wa'adin shekaru biyu kacal da aka dibawa kasar ta shirya gasar, bayan da kasar Zambia ta nuna ba za ta iya ba sabo da matsalolin kudade.
Daga karshe shugaba Guebuza ya yi kira ga 'yan wasan kasashen Afrika da su shirya sosai wajen tinkarar gasar wasannin Olympic na 2012 da za'a gudanar a birnin London, da kuma gasar wasannin kasashen Afrika karo na 11 da aka tsara gudanarwa a kasar Brazzaville a 2015.
A yayin gasar na bana da aka kammala a kasar Mozambique, kasar Afrika ta Kudu ce kan gaba inda ta samu tagulla 40, azurfa 55 da kuma zinare 61, sai kuma mai biye mata Najeriya wadda ta samu zinare 31, azurfa 28 da kuma tagulla 39.
Ita kuma mai masaukin baki kasar Mozambique ta tashi da kyautuka 12 wadanda suka kunshi azurfa 4 da kuma tagulla 8 (BAGWAI).