Armando Emílio Guebuza ya fadi haka ne a yayin da yake karbar takardar nadi ta jakadan Sin da aka tura Mozambique, Li Chunhua a wannan rana, inda ya furta cewa, Sin aminiyar kasar Mozambique ce bisa manyan tsare-tsare. Kasashen biyu sun dade suna zumunci tsakaninsu. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, hadin gwiwa tsakaninsu na kara zurfafa. Gwamnatin kasar Mozambique ta amince da sakamakon hadin gwiwa da dangantakar da ke tsakaninsu. Bangarorin biyu na fatan karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannin bunkasa kasar Mozambique bisa manyan tsare-tsare.
A nasa bangare, jakada Li Chunhua ya bayyana cewa, zai yi iyakacin kokari wajen sa kaimi ga hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu, da bunkasa dangantakar abokantaka tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.