Shugaba Guebuza ya fadi haka ne a wajen taron murnar shiga sabuwar shekara da jakadun kasashe daban daban dake kasar Mozambique suka kira, inda ya ce tsarin da kasashen duniya suke bi wanda ya shafi tattalin arziki da sauran fannoni ya yi wa kasashe dake tasowa tarnaki a kokarinsu na samun ci gaba cikin sauri. A cewarsa, gwamnatin kasar Mozambique na fatan ganin kungiyar cinikayya ta duniya (WTO) ta gagauta cimma nasara a shawarwarin zagayen Doha.
Yayin da yake waiwayen yadda aka gudanar da harkokin mulki a shekarar 2012, shugaban ya ce zaman lafiya, shawarwari, da zama tare cikin jituwa sun kasance harsashin al'adun kasar Mozambique a fannin siyasa. Kan wannan tushe ne kasar ta samu damar karfafa hadin kan kabilu daban daban da ke kasar, inganta tsarin da ake bi na Demokuraddiya, gami da tabbatar da zaman karko a fannin manyan tsare-tsaren tattalin arziki.
Haka zalika, shugaba Guebuza ya yi alkawarin cewa, kasar Mozambique za ta tsaya kan manufar yin shawarwari don tabbatar da masalaha tsakanin kabilu daban daban, ta yadda za ta taimakawa duniya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. (Bello Wang)