Ganin hakan ne ya sa gwamnatin kasar ta sanar da cewa, wadannan yankunan sun shiga halin ko ta kwana sabo da cikowar ruwa.
Gwamnatin kasar ta yi kira ga mahukuntan wurare daban-daban da su janye al'ummominsu daga wadannan yankuna masu hadari, sannan ya kamata su taimaka masu yadda ya kamata.
Tun shigowar lokacin damina a kasar, an samu ambaliyar ruwa a lokuta da dama, musamman ma a yankunan tsakiya da kudancin kasar.
Ya zuwa yanzu, mutane 40 sun rasa rayukansu, yayin da wasu kusan dubu 30 sun rasa gidajensu. (Maryam)